A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza daga Nijeriya, fitattun matasa masu ta'ammuli da kafofin sada zumunta Adam Mohd Bichi, Aliyu Dahiru Aliyu da Salisu Yakubu RN RNT sun bayyana ra’ayoyinsu daban-daban kan rikicin Gabas ta Tsakiya, dangantakar Saudiyya da Iran, yaƙin Yemen da kuma yadda ake amfani da bambancin mazhabobi wajen fahimtar rikice-rikicen siyasa. A rubuce-rubucensu, sun mayar da hankali kan rawar shugabannin siyasa, tasirin farfaganda da muhimmancin bambance tsakanin Musulunci da manufofin gwamnatocin ƙasashen Musulmi.
Adam Mohd Bichi: Farfaganda da amfani da saɓanin mazhabobi
A cikin rubutunsa a shafinsa na Facebook mai taken “Gabas Ta Tsakiya Ta Buɗe”, Adam Mohd Bichi ya yi nazari kan yadda bambancin fahimtar addini tsakanin Shi’a da Ahlus-Sunnah zai iya rikidewa zuwa ƙiyayya, musamman idan aka yi amfani da shi wajen cimma manufofin siyasa.
Matashin ya rarraba mutane zuwa rukuni biyu: waɗanda ba su da ilimi kan wani batu kuma za su iya fahimtarsa idan aka yi musu bayani, da kuma waɗanda suka riga suka kafe a ra’ayinsu har ba sa son karɓar wata hujja da ta saɓa da abin da suka yi imani da shi.
A cewarsa, rikice-rikicen da suka faru a tsakanin ƙungiyoyin Kiristoci, musamman Orthodox da Roman Catholic, suna nuna cewa saɓanin addini ba lallai ne ya zama sanadin ci gaba da faɗa ba. Ya yi nuni da cewa sauye-sauyen zamantakewa da rage tsaurin fahimta na iya taimakawa wajen samun zaman tare.
Adam Mohd Bichi ya kuma yi magana kan dangantakar Iran da Saudiyya kafin da bayan juyin juya halin Musulunci na Iran a shekarar 1979. Ya bayyana ra’ayinsa cewa, amfani da saɓanin mazhabobi wajen ƙara gaba tsakanin ƙasashen biyu ya taimaka wajen tsananta rikicin yankin. Inda ya nuna cewa kafin juyin juya halin Musulunci na Iran, Iran da Saudiyya suna da kyakkyawar alaƙa, saboda shuwagabannin kasashen biyu a lokacin suna da halayya iri ɗaya, amma bayan juyin juya halin Musulunci sai alaƙar ta sauya.
Marubucin ya ƙara da cewa Saudiyya tana da matsayi na musamman a idon al'ummar Musulmi saboda kasancewar Makka da Madina a cikinta. A ganinsa, wannan matsayi na iya zama hanyar da ake amfani da ita wajen samun goyon bayan jama'a ko kuma gabatar da rikicin siyasa a matsayin hari kan Musulunci.
A ɓangaren Yemen, Adam Mohd Bichi ya soki abin da yake gani a matsayin amfani da batun wurare masu tsarki wajen farfaganda a lokacin rikici. Ya yi nuni da cewa yaƙin da ya daɗe tsakanin Saudiyya da Yemen ya jawo asara mai yawa, kuma ya yi gargaɗin cewa faɗaɗa rikicin Gabas ta Tsakiya na iya jawo ƙarin matsaloli ga yankin.
Aliyu Dahiru Aliyu: Kare mutuncin mumini da sukar farfaganda
A nasa rubutun, Aliyu Dahiru Aliyu ya mayar da hankali kan muhimmancin rayuwar ɗan Adam a Musulunci da kuma abin da ya kira amfani da wurare masu tsarki wajen gina farfaganda ta siyasa.
Ya ambaci ruwayar da ke nuna girman alfarmar mumini a wurin Allah, yana mai cewa da mutane sun fi fahimtar muhimmancin wannan koyarwa, da za a fi mayar da hankali kan kare rayuka da guje wa zubar da jini.
Aliyu ya kuma yi suka ga abin da yake gani a matsayin saɓani tsakanin nuna damuwa kan hare-haren da suka shafi Saudiyya da kuma irin wahalhalun da al'ummar Yemen suka fuskanta a tsawon shekarun yaƙin. A ra’ayinsa, bai kamata a mayar da hankali kan lalacewar kadarori da kamfanoni kawai ba, alhali akwai tambayoyi masu muhimmanci kan rayukan fararen hula da barnar yaƙi.
Marubucin ya kuma yi zargin cewa wasu masu magana kan rikicin na iya amfani da batun Makka da Madina wajen ƙarfafa farfaganda. Ya bayyana damuwarsa cewa ana iya gabatar da hare-hare kan Saudiyya a matsayin hari kan Musulunci gaba ɗaya, ba tare da bambance tsakanin ƙasar, gwamnatinta da addinin Musulunci ba.
Babban saƙon rubutunsa shi ne cewa ya kamata a yi la'akari da darajar rayuwar ɗan Adam da koyarwar addini yayin nazarin rikice-rikicen siyasa, maimakon a fifita muradun ƙasashe ko kamfanoni a kan jinƙai da adalci.
Salisu Yakubu RN RNT: Bambance Saudiyya da shugabanninta
Salisu Yakubu RN RNT ya bayyana ra’ayinsa kan rikicin Saudiyya da dakarun Houthi, inda ya yi tambayoyi kan amfanin ci gaba da rikici da kuma illolinsa ga al'ummar yankin.
Matashin marubucin ya nuna damuwarsa kan halin tsaro da shugabannin Saudiyya za su iya fuskanta sakamakon hare-haren da ake kai wa ƙasar. Ya kuma yi magana kan tasirin dangantakar Saudiyya da Amurka, musamman a fannin sayar da makamai da haɗin gwiwar tsaro. Inda ya bayyana cewa Allah ne kaɗai ya san irin makudan kuɗaɗen da Amurkan ke samu daga Saudiyyar a sakamakon wannan yaƙin na makamai.
A cikin misalin da ya bayar, Salisu ya kwatanta rikicin da yiwuwar wata ƙasa ta kai wa maƙwabcinta hari saboda saɓanin siyasa, sannan a sa ran cewa wanda aka kai wa harin zai zauna ne kawai ba tare da mayar da martani ba. Inda ya bayyana hakan a matsayin abin da ya saɓa wa hankali.
Salisu Yakubu ya kuma soki abin da yake gani a matsayin haɗa Saudiyya da Musulunci kai tsaye, yana mai cewa bai kamata a ɗauki duk wani hari kan ƙasar a matsayin hari kan addinin Musulunci ba.
A ra’ayinsa, ya kamata a bambance tsakanin al'ummar Saudiyya, wurare masu tsarki da ke cikin ƙasar, da kuma shugabannin siyasar da ke tsara manufofinta. Ya bayyana cewa ƙaunar da Musulmi suke yi wa Makka da Madina ba ta kamata ta hana su tantance ayyukan shugabanni ko tambayar sakamakon manufofinsu ba.
Marubucin ya kammala da kira ga Musulmi da su guji abin da yake gani a matsayin jahilci da son jin labaran da suka dace da ra’ayoyinsu kawai, tare da buƙatar su duba batutuwan siyasa bisa hujja da kuma bambance addini da ayyukan masu mulki.
Ra’ayoyi daban-daban, tambaya guda
Duk da bambancin salon rubutunsu, Adam Mohd Bichi, Aliyu Dahiru Aliyu da Salisu Yakubu RN RNT sun tabo batutuwan da suka shafi dangantakar addini da siyasa, rawar farfaganda da kuma illolin rikice-rikicen Gabas ta Tsakiya.
Adam Mohd Bichi ya fi mayar da hankali kan yadda ake amfani da saɓanin mazhabobi wajen ƙarfafa rikicin siyasa; Aliyu Dahiru Aliyu ya jaddada muhimmancin alfarmar rayuwar mumini da sukar abin da yake gani a matsayin farfaganda; yayin da Salisu Yakubu RN RNT ya fi karkata ga bambance Saudiyya da shugabanninta, tare da tambayar amfanin rikici da illolinsa.
Rubuce-rubucen sun nuna yadda marubutan suka yi amfani da ra’ayoyinsu wajen nazarin rikicin yankin. Wannan dai yana nuna yadda al'umma musamman matasa suka fara gano irin badaƙalar da gidan sarautar na Saudiyya ke yi tare da fakewa da wuraren masu tsarki.
Mai rahoto: Musa Shuaibu
Ra'ayinka